Akwai magunguna kala biyu da ake amfani da su domin zubar-da-ciki: mifepristone da kuma misoprostol Cubar-da-ciki da kwayoyi yana aiki sosai idan har duka waɗannan magungunan an yi amfani da su. Har wa yau, idan ba a samu mifepristone ba, to misoprostol ma shi kaɗai zai yi aiki domin kawar da ciki kuma hakan shi ma bashi da wata matsala.
Zaɓi in kina son ki sami sani dangane da sharuɗa na zubar-da-ciki cikin sauƙi tare da mifepristone da kuma misoprostol ko kuma misoprostol shi kaɗai.
Kafin farawa, fara karanta shawarwarinmu a kai Kafin Yin Amfani Da Kwayoyin. Ki tabbatar:
Domin zubar-da-ciki da kwayoyin mifepristone da kuma na misoprostol, kina da buƙatar ki sha kwaya ɗaya 200mg da kuma huɗu zuwa takwas 200mcg na kwayar mifepristone. Kuma kina da buƙatar kwayar kashe raɗaɗi a tare da ke, kamar ibuprofen, domin ya taimaka wajen sarrafa zafin. Acetaminophen da paracetamol ba sa aiki a kan raɗaɗi yayin zubar-da-ciki saboda haka ba a yarje musu ba.
Ga yadda ake amfani da mifepristone da misoprostol a tare domin kawar da juna-biyu:
Haɗiyi kwaya ɗaya 200mg ta mifepristone tare da ruwa.
Jira zuwa awa 24-48.
Sanya kwayar misoprostol guda huɗu (200 mcg ko wacce) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 yayin da suke narkewa. Ba zaki yi magana ko cin wani abu ba a tsawon wannan mintuna 30, saboda haka yana da kyau ki samu wurin da yake ba hayaniya inda ba za a dameki ba. Bayan mintuna 30, sai ki sha ruwa sannan ki haɗiye duk abinda yayi saura na kwayar. Sannan wannan shine lokacin da ya dace ki sha maganin kashe raɗaɗi kamar ibuprofen, domin murɗa zata fara nan da nan.
Zaki fara zubar da jini da kuma murɗeɗeniya a cikin awanni 3 na amfani da kwayar misoprostol guda huɗu.
Bayan awa 24 da shan kwayoyi huɗu na misoprostol, idan baki fara zubar da jini ba, ko baki da tabbacin cikin ya zube, sanya wasu kwayoyin huɗu na misoprostol a kan harshenki. Ajiyesu tsawon mintuna 30 yayin da suke narkewa. Bayan mintuna 30, sai ki sha ruwa sannan ki haɗiye duk abinda yayi saura na kwayar.
Ki san me kuma za a jira aukuwarsa bayan shan mifepristone da kuma misoprostol a nan.
Idan kin fuskanci mummunar murɗawa, to kwayar ibuprofen kyakkyawan magani ne domin magance raɗaɗi. Zaki iya sayan ibuprofen kimanin 200 mg a wurin saida magani (ba tare da takardar izinin likita ba)a ƙasashe da dama. Sha kwaya 3-4 (200 mg ko wanne) a duk awanni 6-8. Idan kina buƙatar ƙarin abin kashe raɗaɗi, zaki iya nan ma amfani da kwaya guda 2 na Tylenol (325 mg) duk awanni 6-8.
Idan kin damu da hanyar zubar-da-ciki sannan kina buƙatar ƙarin taimako, zaki iya saduwa da abokai a www.safe2choose.org, www.womenhelp.org or www.womenonweb.org.
Idan kin yi amfani d kwayoyin zubar-da-ciki na mifepristone da misoprostol, kuma ta yiwu bakya son zuwa cibiyar kula da lafiya domin ziyarar bincikawa. Waɗannan magungunan suna da aminci sosai har ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yarje cewa kina da buƙatar ziyarar bincikawar ne kaɗai idan:
Kafin farawa, fara karanta shawarwarinmu a kai Kafin Yin Amfani Da Kwayoyin. Ki tabbatar:
Idan mifepristone baya samuwa a inda kike, zaki iya amfani da misoprostol shi kaɗai domin kawar da ciki.
Domin zubar-da-ciki da misoprostol kaɗai, kina da buƙatar shan kwayoyi guda goma sha biyu 200mcg na misoprostol. Kuma kina buƙatar samun kwayoyin kashe raɗaɗi a tare da ke, kamar ibuprofen, domin sarrafa raɗaɗin. Acetaminophen da paracetamol ba sa aiki a kan raɗaɗi yayin zubar-da-ciki saboda haka ba a yarje musu ba.
Ga yadda ake amfani da misoprostol shi kaɗai domin kawar da juna-biyu:
Sanya kwayar misoprostol guda huɗu (200 mcg ko wacce) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 yayin da suke narkewa. Ba zaki yi magana ko cin wani abu ba a tsawon wannan mintuna 30, saboda haka yana da kyau ki samu wurin da yake ba hayaniya inda ba za a dameki ba. Bayan mintuna 30, sai ki sha ruwa sannan ki haɗiye duk abinda yayi saura na kwayar. Sannan wannan shine lokacin da ya dace ki sha maganin kashe raɗaɗi kamar ibuprofen, domin murɗa zata fara nan da nan.
Jira tsawon awa 3.
Sake sanya wasu kwayoyin misoprostol guda huɗu (200 mcg) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 har sai sun narke.
Jira tsawon wasu awannin 3.
Sake sanya wasu kwayoyin misoprostol guda huɗu (200 mcg) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 har sai sun narke.
Zaki fara zubar da jini da murɗeɗeniya yayin shan kwayoyin. Ki tabbata kin shanye duka kwayoyi 12 ɗin ko da kin fara zubar da jini kafin ki gama shanyesu.
Ki san me kuma za a jira aukuwarsa bayan shan misoprostol a nan.
Idan kin fuskanci mummunar murɗawa, to kwayar ibuprofen kyakkyawan magani ne domin magance raɗaɗi. Zaki iya sayan ibuprofen kimanin 200 mg a wurin saida magani (ba tare da takardar izinin likita ba)a ƙasashe da dama. Sha kwaya 3-4 (200 mg ko wanne) a duk awanni 6-8. Idan kina buƙatar ƙarin abin kashe raɗaɗi, zaki iya nan ma amfani da kwaya guda 2 na Tylenol (325 mg) duk awanni 6-8.
Idan kin damu da hanyar zubar-da-ciki sannan kina buƙatar ƙarin taimako, zaki iya saduwa da abokai a www.safe2choose.org, www.womenhelp.org or www.womenonweb.org.
Idan kin yi amfani da misoprostol, kusan ba ki da buƙatar ziyartar cibiyar kula da lafiya domin ziyarar bincikawa. Waɗannan magungunan suna da aminci sosai har ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yarje cewa kina da buƙatar ziyarar bincikawar ne kaɗai idan:
Wannan rukunin yanar gizon na iya buƙatar cookies da ba a san su ba da kuma sabis na wasu daban don yin aiki yadda ya kamata. Kuna iya karanta Sharuɗɗanmu & Yanayi da Manufofin Sirri . Ta hanyar ci gaba da amfani da wannan rukunin yanar gizon kuna bamu yardar ku don yin hakan.